<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>269</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Zumuntar Masu Bi da daɗi kamar me!
 Ba za a ga irinsa ba, sai can wurin Kristi.

[V2]
 2) Kadan wani Mai Bi ya je don wa'azi,
 Kome nisan tafiyarsa, ba za mu manta ba.

[V3]
 3) Sai binsa za mu yi ta wurin roƙonmu.
 Da ƙauna za mu raka shi, mu ƙarfafa shi kuwa.

[V4]
 4) Ko cikin ƙunci ne, ko wurin hatsari,
 Ko ciwo ne, ko lafiya, ba za mu fasa ba.

[V5]
 5) Idan ya dawo fa, murnar da za mu yi
 Ba za a ga irinta ba sai wurin Masu Bi.

[V6]
 6) Can wurin Yes dai inda ba rubuwa,
 Can za mu gai da junanamu, mu gode har abada,</lyrics>
<title>Zumuntar Masu Bi da Daɗi Kamar Me LW269</title>
<author>Mason, Lowell (1792-1872), Fawcett, John (1740-1817)</author>
</song>